KALLI CHANJIN DA YARONDA IYAYENSA SUKA DAURE TARE DA DABBOBI YASAMU BAYAN WATANNI
KALLI CHANJIN DA YARONDA IYAYENSA SUKA DAURE TARE DA DABBOBI YASAMU BAYAN WATANNI Gwamnatin jihar Kebbi ta mika Jibril Aliyu ga iyayensa, yaron dan shekara 11 da mahaifinsa tareda kishiyar mahaifiyarsa suka daure tare da dabbobi da yunwa tsawon shekaru biyu, a unguwar Badariya da ke cikin garin Birnin Kebbi. Idan dai za a iya tunawa, a ranar 9 ga watan Agusta, 2020, gwamnatin jihar ta yi alkawarin yi wa yaron magani gaba daya, bayan da aka daure shi da sarka da mahaifinsa da kishiyar mahaifiyarsa suka yi masa. Bayan daure yaron da sarka, an gano cewa yana rayuwa da dabi’a irin ta dabbobi, kuma wannan ya tilasta masa cin abincin dabbobi dakuma kashin dabbobi, ba tare da ruwa ba, yayin da yake yawan cin najasarsa a matsayin hanyar tsira da rayuwarsa. Da yake mika yaron ga iyayensa, babban daraktan kula da lafiya kuma babban sakatare na asibitin tunawa da Sir Yahaya, Dakta Aminu Haliru Bunza, ya ce sama da kwararrun likitoci 20 ne suka halarci wurin yaron yayin da yake zaune a asibit...